- Tunin Muka Kaddamar Da Bincike Kan Bacewar Bindigoginmu, In Ji Shi
- Wai Me Kwamishinan Ke Boyewa – Dogara Ya Tambaya
Kwamishinan ‘Yansandan Jihar Bauchi Umar Mamman Sanda, ya bayyana cewar tunin suka maida hankali wajen gudanar da bincike kan ikirarin da wani ya yi na cewa zai kashe tsohon Kakakin Majalisar wakilai ta tarayya, Rt. Hon. Yakubu Dogara da wasu mutum uku.
Kan hakan, kwamishinan ya ce suna gudanar da ayyukansu ne yadda ya dace kuma za su fitar da hakikanin abun da ya faru. Sai dai ya nuna cewa ba su tabbatar da cewa rayuwar Dogaran na cikin hatsari ba, illa dai sun kama wanda ya furta cewa zai sayi bindiga ne don kashe Dogaran tare da dan sandan da ya saci bindigar da nufin saidawa mutumin.
Kwamishinan wanda ke maida bayani kan wasikar korafi da Yakubu Dogara ya aike wa Shugaban ‘yansanda na kasa Usman Baba Alkali inda ke shaida masa cewar rayuwarsa na cikin hatsari domin wani mai suna Barau Joel Amos na son sayan bindigogi a hannun wasu ‘yan sanda Insifekta Dakat Samuel da Insifekta Auwalu Mohammed domin ya kasheshi shi da wasu mutum uku.
Sauran wadanda Amos ke son kashewa a vewar Dogara har da shugaban CAN na karamar hukumar Tafawa Balewa, Rabaran Markus Musa, Barr. Istifanus Bala Gambar da wani Mr. Emmanuel (Shugaban NL, na T/Balewa).
Said dai kwamishinan ‘yansandan ya ce: “Abun da ya faru shine mun samu bayanai na sirri cewa lallai akwai wani dan sandanmu da yake son zai sayar da bindiga. Sai muka je muka nemoshi daman an ba mu labarin cewa har ya sanya bindigun a cikin motarsa, sai muka je muka sameshi muka ce waye mai motar ya ce shi ne, muka binciki motar muka samu bindigogi.
“Aka tambayeshi waye ya baka bindigogin ya ce ya dauko ne zai sayar. Bindigogin ‘yansandan za ka sayar? Ya ce eh. Muka kamashi muka fara bincike, a cikin binciken ya kama sunan wani dan uwansa wanda suke wuri daya. Shi wanda muka kaman da farko ya bamu labari ya ce mana wani mutum ne dan can yankin Tafawa Balewa shi ne yake so ya sayi bindiga shi ya sanya ya dauko masa bindigogi, ya fada mana waye sai muka je muka kamo wancan din.
“Da muka kama shi (na biyun) shi ma muka ce ya aka yi ya ce gaskiya ne yana neman bindiga ne saboda gaskiya wani abun al’ajabi ya sameshi akwai dan tarzomar da ya tashi a can wajajen Tafawa Balewa, Bogoro a kan kaddamar da littafin da aka rubuta na Baba Gwanto a watan Disamban da ya gabata an kona masa gidaje da na sauran jama’a.
“An kona maka gidaje shine meye? Ya ce a’a ai su Dogara da wadansu mutane ne, shi ya sa yake neman bindiga don ya kashesu.”
“Ka san ba kasafai ne idan dan adam ya yi laifi zai fito ya fada maka gaskiyar abun da ya yi ba, sai ka masa ‘yan hikima kafin nan sai gaskiyar ta fito. Bayan da aka yi haka din mun kaddamar da bincike a kan wannan batun.”
Kwamishinan ya kuma ce, bayan hakan ma kan batar bindigoginsu nan take ya bada umarnin cewa dukkanin wuraren ajiye makamansu a je a kirga musu makamai a bincika menene babu, “Sai muka samu bayan wadannan bindigogi biyun da muka kama wasu ma babu su sun bata. Nan fa bincike ya fadada. A yanzu maganar da nake maka akwai mai kula da wajen ajiye makamanmu wanda ya yi ritaya shekaru biyu zuwa uku da suka wuce a shekarar jiya (ranar Juma’a) aka kamashi domin mun yi ta nemansa ba mu sameshi ba.
“Na ce shi ma a kulleshi, muna nan muna kan bincike kwatsam kawai sai muka ga shi (Dogara) ya rubutu wasika. Har yana zargin cewa ba mu kirashi mun gaya mishi ba, ba mu tabbatar ba, bayan maganar da shi wannan mutumin ya yi ba mu sake samun wani tabbacin lallai cewa rayuwarsa (Dogara) na cikin barazana ba, ko kuma wannan bindigar da aka sayen an yi ne saboda a kasheshi ba, wannan babu tabbaci a cikinsa. Kuma mu ba za mu fito mu yi magana wa duniya ce ga abun da ke akwai ba kuma ya zo daga baya bincike ya nuna mana ba haka yake ba.
“Saboda haka wannan magaanar ba daidai ba ne kuma mu ‘yansanda muna nan muna cigaba da bincikenmu za mu yi bayani wa jama’a idan muka kammala bincikenmu. Babu wani abun boyewa a ciki,” a cewar kwamishinan.
Umar Mamman Sanda ya ce hatta zuwa ga wannan matakin ma bisa kokarinsu da jajircewarsu ne aka kawo ga wannan, in ba haka ba ma ai ba za mu sani ba.
Kwamishinan ya nemi jama’a da su ba su lokaci domin su kammala bincike tare da fito da bayanin hakikan abubuwan da suka faru.
Kwamishinan ya ce karar da Yakubu Dogara ya kai wajen shugaban ‘yansandan na kasa ba matsala ba ne, amma bai kamata ya nuna cewa su ‘yansandan a jihar Bauchi ba su yi abun da kamata ba ba daidai bane domin har yanzu suna bincike kan bayanin da suka samu da yadda za su tabbatar da shi, “Bayani ne muka samu daga wajen mutum daya, kuma babu wani mutum ko wasu da muka samu suka tababtar mana da wannan maganar cewa lallai a hakan take.
“Sai mun bai wa wasu kwararrunmu wadanda suke bincike a kan maganar bindigogi da maganar kashe mutane su ne za su gaya mana cewa eh lallai wannan maganar haka ne kuma an samu wane da wane a ciki sai mu fito mu fada wa duniya mu yi bayani ga abun da ke akwai, ko shi kansa (Dogara) ba mu kai ga inda za mu tambaya ko akwai wani barazana da ya gani a rayuwarsa kafin wannan abun don mu mu sani sannan mu fito da bayananmu na bincike,” kwamishinan ya karkare.
A gefe guda kuma Yakubu Dogara ya nuna mamakinsa kan yadda kwamishinan da kansa ya tabbatar da cewa sun kama dan sanda guda da bindigogi da yake kokarin sayarwa da kuma wanda suka kama da ya shaida da bakinsa cewa na son sayen bindiga ne don ya kashe shine amma kuma hakan bai zama hujja da zai tabbatar rayuwar tasa na cikin hatsari ba.
Dogaran ta bakin kakakinsa Turaki Hassan ya yi tambaya da cewa, “Akwai wata hujjar da ta wuce wanda ake zargi da kansa ya bayyana batu da bakinsa? Wai meye kwamishinan yake kokarin rufewa ne?.
Ya kuma sake yin tambayar cewa don meye kwamishinan bai bayyana wanda suka cafke da bisa zargin kamasa da bindigogin ba.?