Wata babbar kotu a jihar Kano ta bayar da umarnin tsare Ogugua Christopher, mai gidan marayu da ke Asaba a jihar Delta, bisa zargin satar kananan yara da safarar kananan yara da aka ce an sato su ne daga jihar Kano zuwa Asaba.
Ana tuhumar Ogugua ne tare da Hauwa Abubakar da Nkechi Odlyne akan tuhume-tuhume 15 da suka hada da hadin baki da kuma sace yara, wanda aka ce ya saba wa sashi na 97 da 273 na kundin laifuffuka na jihar Kano da sashe na 32(5) na dokar yara da matasa.
A cewar mai gabatar da kara, wadanda ake tuhumar sun sace yara da dama tsakanin watan Yuni 2016 zuwa Disamba 2021 tare da sayar da su a jihar Delta.
A zaman na ranar Talata, lauyan masu shigar da kara, Salisu Muhammad-Tahir, ya shaida wa kotun cewa biyu daga cikin wadanda ake tuhumar, Abubakar da Odlyne, ba a samu gabatar da su a gaban mai sharia ba duk da kokarin tilasta musu halartar zaman.
Muhammad-Tahir ya ce “Mun yi iya bakin kokarinmu don tabbatar da kawo su gaban mai shari’a, amma muna neman afuwar kotu,” in ji Muhammad-Tahir, inda ya bukaci alkalin da ya dage sauraron karar tare da tsare Ogugua a gidan yari har sai an gabatar da wadanda ake nema.
Lauyan wanda ake kara, Gideon Uzo, ya roki kotun da ta bar wanda yake karewa ya ci gaba da zama a hannun hukumar hana fataucin mutane ta kasa (NAPTIP) maimakon a tura shi gidan gyaran hali.
Sai dai alkalin kotun, Mai shari’a Amina Adamu-Aliyu, ta ki amincewa da bukatar, inda ta bayar da umarnin a ajiye wadanda ake zargin a gidan gyaran hali. Ta kuma umurci hukumar ta NAPTIP da ta gabatar da mutanen biyu da ba su halarci zaman kotun ba.
An dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 27 ga watan Oktoba.