Gwamnatin Tarayya ta bayyana matukar damuwarta kan yadda ake samun jinkiri a kotuna wajen hukunta mutanen da ake zargi da aikata laifin fyade, inda ta ce daga cikin mutane sama da 11,000 da ake zargi, 33 kacal aka yanke wa hukunci.
Ministan kula da harkokin mata, Pauline Tallen, ta bayyana haka lokacin da take jawabi wajen wani taro da aka shirya a Abuja a karkashin Majalisar Dinkin Duniya domin fadakar da jama’a illar cin zarafin mata.
- ‘Yansanda Sun Cafke Mutum 909 Kan Zargin Aikata Manyan Laifuka A Adamawa
- Kumbon Shenzhou-15 Na Kasar Sin Ya Hade Tashar Binciken Sararin Samaniyar Kasar
Tallen ta ce daga cikin wadannan laifuffuka na fyade da aka gani a Najeriya sama da 11,000, an samu rasa rayukan mata 401, yayin da wasu da dama kuma aka raunata su.
Ministar ta danganta al’adu da kin gudanar da bincike daga bangaren jami’an tsaro da rashin taimaka wa wadanda aka yi wa fyaden a matsayin manyan matsalolin dake hana wasu mata kai kara idan suka fuskanci irin wannan cin zarafi, wanda yake karuwa kowace shekara.
Tallen ta bayyana cewar Najeriya ta gaza daukar matakai masu tsauri wajen hana fyade da kuma hukunta wadanda suke cin zarafin mata ta wannan mummunar dabi’ar, ganin yadda suke sulalewa da zaran an kai su kotu.