Wata kotun Entebbe da ke ƙasar Uganda, ƙarƙashin mai shari’a Stellah Maris Amabilis, ta tasa ƙeyar wani matashi ɗan TikTok mai shekaru 21, gidan yari bayan samunsa da laifin wallafa wani bidiyo da aka ce yana cin mutuncin shugaba Yoweri Museveni.
Emmanuel Nabugodi, wanda aka yankewa hukuncin ɗaurin watanni 32 a gidan yari, an gurfanar da shi ne a gaban kotu ranar litinin, bayan ya amsa laifinsa kan wasu tuhume-tuhume huɗu da suka haɗa da kalaman nuna ƙiyayya da yaɗa munanan bayanai game da shugaban ƙasar.
- Shugabannin Sin Da Faransa Sun Rubuta Bayanai Domin Wani Bikin Baje Koli Na Musamman
- Kotu Ta Wanke Kwamishinan Jigawa Daga Zargin Zina
Nabugodi wanda ya shahara wajen wallafa abubuwan barkwanci ya yi wani bidiyon shari’ar izgili da ake yi wa shugaban ƙasa, inda a ciki yake kira da a yi wa Museveni bulala a bainar jama’a.
Sai dai ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama sun nuna rashin jin daɗi kan yadda ake tauye ƴancin faɗin albarkacin baki a ƙasar, tare da zargin shugaban wanda ke kan karagar mulki tun 1986 da rashin lamuntar suka.
Ko a watan Yulin da ya gabata ma an yankewa wani Edward Awebwa, hukuncin shekaru shida kan makamanciyar tuhuma wanda ko a yanzu wasu mutane uku ma suna jiran hukunci kan abubuwan da suka wallafa a shafukansu na sada zumunta.