A ranar Laraba ne wata babbar kotun jihar Kano ta dage ci gaba da sauraron shari’ar da ake yi kan zargin karbar cin hanci da rashawa da ake zargin shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Ganduje, da matarsa Hafsat Ganduje da wasu mutane shida.
Gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da wadanda ake tuhumar ne a gaban kotu a kan tuhume-tuhume takwas da suka hada da cin hanci, almubazzaranci, da karkatar da kudaden jama’a da suka kai biliyoyin naira.
Wadanda ake tuhumar sun hada da Ganduje da matarsa, da Abubakar Bawuro, Umar Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad, Lamash Properties Limited, Safari Textiles Limited, da Lasage General Enterprises Limited.
Mai shari’a Amina Adamu-Aliyu ta jaddada bukatar sanarwa a hukumance yadda ya kamata don yi wa dukkan bangarorin adalci a shari’ar.
Daga bisani ta dage sauraron karar zuwa ranar 20 ga watan Nuwamba, 2024, domin ci gaba da sauraron karar.