Kotun ƙoli a Abuja, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Maryann Anenih, ta ɗage yanke hukunci kan buƙatar tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, da ke neman izinin fita ƙasar waje domin jinya, zuwa ranar 17 ga Yuli, 2025.
Bello da wasu mutane biyu, Umar Oricha da Abdulsalami Hudu, na fuskantar shari’a kan tuhume-tuhume 16 da suka shafi zargin damfara da safarar dukiya da ta kai Naira biliyan 110, tun daga ranar 27 ga Nuwamba, 2024.
- Wasu ‘Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Gidan Sanata Natasha A Kogi
- Gwamnatin Zamfara Ta Tabbatar Da Kashe Manyan Mayakan Bello Turji Fiye Da 100
Lauyansa, Joseph Daudu (SAN), ya shaida wa kotu cewa ya gabatar da buƙatar a saki fasfo ɗin Yahaya Bello domin ya je jinya a Birtaniya, wanda aka gabatar da ita ranar 20 ga Yuni tare da hujjoji 13 da shaidu 22 da Bello ya rattaɓa hannu a kai.
Hukumar EFCC ta ƙi yarda da buƙatar, tana mai cewa hakan na iya jinkirta ci gaban shari’ar. Lauyan hukumar, Chukwudi Enebeli (SAN), ya ce ya kamata a sanar da masu tsaya masa beli kafin ya yi wannan buƙatar, don su yanke shawarar ko za su ci gaba da tsaya masa. Haka kuma, ya ce gabatar da irin wannan buƙata a kotu biyu daban-daban (FCT da FHC) na iya haddasa rikici tsakanin kotunan.
Daudu ya mayar da martani yana mai cewa an sanar da masu tsaya wa Yahaya Bello beli, kuma babu buƙatar sanar da su daban. Ya kuma ce batun “red alert” da EFCC ke ambatawa ba shi da tushe, domin Yahaya Bello bai taɓa karya umarnin kotu ba. Bayan sauraron ɓangarorin biyu, Mai Shari’a Anenih ta ɗage yanke hukunci har zuwa ranar 17 ga Yuli, 2025.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp