Wata kotun majistire da ke Norman’s Land a Ƙaramar Hukumar Fagge a Jihar Kano, ta yanke hukuncin ɗaurin shekara ɗaya ko biyan tarar Naira 100,000 ga wasu matasa biyu da aka samu da laifin wallafa bidiyon batsa a TikTok.
Hukumar tace fina-finai ta Kano ce, ta kama matasan, Ahmad Isa da Maryam Musa, mazauna unguwar Ladanai a unguwar Hotoro, sannan ta miƙa su ga kotu.
- Za A Sake Gurfanar da Blatter Da Platini Kan Zargin Cin Hanci
- NLC Ta Yi Allah-wadai Da Yunƙurin Ƙara Kuɗin Wuta, Ta Yi Barazanar Shiga Zanga-zanga
Lauyan gwamnati, Barista Garzali Maigari Bichi, ya bayyana cewa an same su da laifin haɗa baki da wallafa bidiyon da suka saɓa wa tarbiyya da addini a jihar.
Matasan sun amsa laifinsu, inda aƙkalin kotun, Mai shari’a Hadiza Muhammad Hassan, ta yanke musu hukuncin ɗaurin shekara ɗaya.
Sai dai ta ba su zaɓin biyan tarar Naira 100,000 kowannensu, tare da gargaɗi kan muhimmancin kyautata halayya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp