Wata babbar kotun jihar Kaduna da ke zamanta a Dogarawan ta amince da bayar da belin matashi da ke ake zargi da yin garkuwa da Yayarsa domin karbar kudin fansa a Zariya da ke Kaduna bisa dalilai na rashin lafiya.
Da yake bayani kan belin, Alkalin babbar kotun jihar, Justice Kabir Dabo, ya bayyana cewar wanda ake zargin na fama da matsanancin tari wanda kotu ke ganin mahalarta shari’ar na iya kamuwa da ita domin kuwa duk ranar zaman sauraron kararsa sai ya yi amfani da abun rufe hanci domin yawan yin tarin nasa.
Daga cikin sharadin da kotun ta bayar na belin wanda ake zargin har da cewa mutum mai gida a yankin da kotun take shine zai karbi belinsa kuma dole sai yana da gida da kudinsa ya kai Naira miliyan 10 kuma zai ajiye takardun mallakar gidan, kuma dole sai mai tsaya masa din na da kudin da ya kai miliyan 10 a asusu ajiya na banki.
Alkalin kotun ya ce belin da ya bayar zai ba shi damar neman maganin ciwon da ke damun sa kafin ranar da za a ci gaba da sauraron shaida na karshe daga bangaren masu gabatar da kara. Kotun ta bayar da belin a karkashin sashi na 36(5) na dokar shekarar 1999 da sashi na 174(1) da (2) da (c) na sashin dokar manyan laifuka ta Jihar Kaduna.
Daga nan kotun ta tafi hutu sai ranar 19 ga watan Satumba 2022 kuma shari’ar za ta ci gaba da gudana a ranar 18 ga watan Oktoba, 2022.