Babbar Kotun Jihar Kano, ta bayar da umarnin kama Barista M. A. Lawal, tsohon Antoni-Janar kuma Kwamishinan Shari’a, bayan ya gaza halartar kotu domin gurfana kan tuhume-tuhume da ake masa.
Ana tuhumar Lawal da laifuka huɗu da suka shafi ɓatan da kuɗi da kuma cin amana da suka kai Naira miliyan 240.
Shari’ar tana kuma shafar Abdullahi Umar Ganduje, Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano.
A zaman kotun na ranar Litinin, masu gabatar da ƙara sun sanar da kotu cewa har yanzu ba a miƙa wa Ganduje sammaci ba, duk da umarnin da aka bayar a baya.
Sai dai an aike wa Lawal sammaci amma bai bayyana a kotu ba.
Alƙalin kotun, Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu, ta bayar da umarnin kama Lawal tare da ɗage shari’ar zuwa ranar 6 ga watan Mayu.
A wata shari’a daban, kotun ta kuma bayar da umarnin kama Jibrilla Muhammad, tsohon Manajan Darakta na Kamfanin Zuba Jari da Kadarorin Kano (KSIP), bisa zargin ɓatan Naira miliyan 212.4.
A gefe guda ta sake ɗage zaman wannan shari’a saboda abokin shari’ar tasa, Dauda Sheshe, har yanzu bai karɓi sammaci ba.
An ɗage shari’arsu zuwa ranar 29 ga watan Afrilu.
Dukkanin waɗannan shari’u na da alaƙa da zargin karkatar da kuɗaɗen jama’a yayin da suke rike da muƙaman gwamnati.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp