Mai shari’a Rahman Oshodi na babbar kotun Jihar Legas, ya bai wa EFCC umarni ci gaba da tsare tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele.
Emefiele zai ci gaba da zama a tsare har zuwa ranar Alhamis, lokacin da alkali zai yanke hukuncin kan batun bayar da belinsa.
- Majalisar Dokokin Edo Ta Tsige Mataimakin Gwamnan Jihar
- Emefiele Ya Gurfana A Gaban Kotu Kan Sabbin Zarge-zarge 26
Mai shari’a Oshodi ya yanke hukuncin ne bayan Emefiele da takwaransa, Herry Omoile, sun ki amsa tuhumar da ake musu kan sabbin zarge-zarge 26.
Lauyan Emefiele, Abdulakeem Ladi-Lawal, ya bukaci kotun ta yi wa wanda yake karewa sassauci tare da bayar da belinsa.
Lauyan ya bukaci kotun da ta sanya sharudan beli irin wanda mai shari’a Hamzat Muazu na babbar kotun birnin tarayya Abuja, ya sanya wa Emefiele a baya.
Lauyan EFCC, Rotimi Oyedepo, bai yi suka kan neman belin ba, sai dai ya bukaci alkali ya gindaya wasu sharuda da za su tilasta wa Emefiele gurfana a gaban kotu.
An tuhumi Emefiele da takwaransa kan almundahana da karkatar da kadarorin gwamnati.
LEADERSHIP ta ruwaito yadda EFCC ta gurfanar da Emefiele a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja bisa zargin almundahanar kudade a lokacin da yake gwamnan CBN.