Kotun kolin Michigan, ta ce ba za ta saurari karar da wasu mutane hudu a jihar suka shigar ta neman hana tsohon shugaban Kasar Amurka, Donald Trump, shiga zaben fidda gwani na jam’iyyar Republican a ranar 27 ga watan Fabrairu ba.
Sun bukaci hakan ne saboda rawar da ya taka a harin da aka kai majalisar dokokin kasar a ranar 6 ga Janairun 2021.
- Harin ‘Yan Bindiga: Shettima Ya Kai Ziyarar Jaje Jihar Filato
- Da Sannu Za Mu Farfado Da Manchester United – Jim Ractliffe
Masu shigar da kara dai, sun yi zargin Trump, wanda ke kan gaba cikin jerin masu neman kujerar shugabancin kasae karkaashin jam’iyyar Republican a 2024, ba zai iya zama shugaban kasa ba a karkashin wani tanadi na kundin tsarin mulkin Amurka da ya haramta wa mutane rike mukamai idan aka same su dumu-dumu cikin masu tayar da hankali ga zaman lafiyar Amurka.
Trump a wani sako da ya wallafa a shafinsa na kafafen sada zumunta, ya ce kotun ta musanta abin da ya kira yunkurin da ‘yan jam’iyyar Democrat suka yi na haramta masa kada kuri’a a Michigan.
Hukuncin na Michigan ya banbanta da hukuncin da babbar kotun Colorado ta yanke a makon da ya gabata na hana Trump, shiga cikin masu tsayawa takara, inda Trump ya sha alwashin daukaka kara kan hukuncin Colorado zuwa kotun kolin Amurka.
An tuhumi Trump da hannu wajen yunkurin juyin mulki a zaben 2020 amma ba a tuhume shi da laifin tayar da kayar baya ba, da ya shafi harin ranar 6 ga watan Janairu ba.
Hukuncin da kotun kolin Amurka ta yanke zai iya warware batun sarkakiyar da ke iya bayyana cancantar Trump ko a akasin haka a fadin kasar na tsayawa takara a zaben 2024.