Babbar kotun Jihar Kogi da ke Lokoja ta bayar da umarnin kama shugaban Hukumar Yaki Da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa, tare da tsare shi a gidan yarin Kuje.
Mai shari’a Rukayat Ayoola ta ce tsare shi a gidan yarin Kuje saboda ya ki bin umarnin kotun.
- Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Dakatar Da CBN Da Buhari Ƙara Wa’adin Maye Tsoffin Kuɗi
- An Samar Da Damar Dawo Da Zirga-zirga A Dukkan Fannoni A Tsakanin Hong Kong Da Babban Yankin Kasar Sin
Ayoola ta kuma umurci Sufeto-Janar din ‘yansanda da ya tabbatar da bin doka da oda saboda shugaban na EFCC ya raina kotun.
Alkalin kotun ta ce a tsare shi na tsawon kwanaki 14 masu zuwa.
A hukuncin da ta yanke, alkalin ta amince da bukatar a ci gaba da tsare Bawa a gidan yari saboda ya ki bin hukuncin da kotu ta yanke a ranar 30 ga Nuwamba, 2022.
An umarci shugaban na EFCC da ya gabatar da wanda ya shigar da karar, Ali Bello.
Lauyan wanda ya shigar da karar, Sumaila Abbas, ya maka Bawa kotu bisa kama shi da tsare Bello ba bisa ka’ida ba, inda kotu ta yanke masa hukunci, sai dai EFCC ta gurfanar da shi a gaban kuliya bisa zargin karkatar da kudade kwanaki uku da yanke hukuncin.
Amma, an ki amincewa da bukatar EFCC na ware da kuma dakatar da aiwatar da hukuncin saboda rashin cancanta.