Kotun Tarayya dake Kaduna ta yanke hukunci kan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da wasu mutum biyar, inda ta umarci a biya diyya har Naira miliyan 900 ga wasu dattawan al’ummar Adara bisa kame su ba bisa ƙa’ida ba a shekarar 2019.
Alƙaliya Hauwa’u Buhari ce ta yanke hukuncin a ranar Talata, inda ta goyi bayan ƙarar da Awemi Dio Maisamari da wasu dattawa takwas na yankin Kudancin Kaduna suka shigar bayan kisan Sarkin gargajiyarsu, Dr. Raphael Maiwada Galadima. Dattawan sun shafe lokaci a tsare ba tare da gabatar da su gaban kuliya ba.
- Ministoci: Majalisar Dattijai Ba Ta Tabbatar Da Tantance Elrufai, Okotete Da Danladi Ba
- Fitaccen Fastan Kaduna Rabaran Azzaman Ya Mutu A Haɗarin Mota
Kotun ta yi watsi da ƙalubalantar hurumin kotun da wanda ake ƙara suka yi, inda suka ce ƙarar ba ta shafi haƙƙoƙin ɗan Adam ba kai tsaye, amma Alƙaliya Hauwa ta ce akwai hurumin kuma hujjojin rashin hurumin ba su da tushe balle makama.
An gano cewa Nasir El-Rufai, wanda aka kai ƙara a matsayin mutum (ba gwamna ba), yana da hannu kai tsaye wajen bayar da umarnin cafke waɗannan dattawa. Wannan hukunci ya zama tamkar yaudara ko rainin hankali ga masu rike da madafun iko.
Lauyan waɗanda suka kai ƙarar, Gloria Mabeiam Ballason, wacce ke jagorantar tawagar lauyoyin, ta bayyana hukuncin a matsayin wata gagarumar nasara wajen tabbatar da adalci da kare haƙƙoƙin bil’adama, inda ta ce, “Wannan hukunci na nuni da cewa koda bayan kammala wa’adin mulki, za a iya hukunta shugabanni idan sun take doka.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp