Kotun Tarayya da ke Lokoja, Jihar Kogi, ta bayar da umarnin dakatar da Hukumar Zaɓe ta ƙasa (INEC) daga karɓar kowace buƙatar da aka gabatar domin fara shirin kiranye ga Senata Natasha Akpoti-Uduaghan daga Majalisar Dattawa.
Haka kuma, kotun ta hana ma’aikatan INEC, da wakilansu, ko duk wani wanda ke da hannu daga karɓar ko yin aiki da kowace buƙata da ke ɗauke da sunayen ƙarya daga mutanen mazaɓar Kogi ta tsakiya, sannan ta hana gudanar da kowanne zaɓe ko taro kan lamarin har sai kotu ta yanke hukunci.
- Kwamitin Majalisa Ya Yi Watsi Da Ƙorafin Da Natasha Ta Shigar A Kan Akpabio
- Majalisar Dattawa Ta Dakatar Da Sanata Natasha Na tsawon Watanni 6 Saboda Rashin Da’a
An bayar da wannan umarnin ne bayan buƙatar gaggawa da Anebe Jacob Ogirima da wasu mutane huɗu daga yankin Kogi ta tsakiya, waɗanda suka yi rajista a matsayin masu zabe suka yi. Buƙatar ta samu wakilcin lauya Smart Nwachimere, na West-Idahosa, SAN & Co., inda kotu ta ɗage shari’ar zuwa 6 ga Mayu, 2025, don samun rahoton aikawa da gayyata da kuma ci gaba da sauraron shari’ar.
A cikin martani ga wannan hukunci, wata ƙungiya mai suna, Action Collective, ta yabawa kotu bisa wannan umarnin, inda shugaban ƙungiyar, Dr. Onimisi Ibrahim, ya ce wannan umarnin zai ƙara bayyana rashin biyayya daga wasu mutanen da ke goyon bayan shirin ƙoƙarin cire Natasha daga Majalisar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp