Wata babbar kotu a Kano ta yanke wa shahararren mai kwalliya, Abdullahi Musa Hussaini (wanda aka fi sani da Amuscap), hukuncin ɗaurin wata shida a gidan yari kan laifin liƙi da taka kuɗin Naira yayin bikin aurensa a watan Disamba.
An yanke masa hukuncin ne bayan ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, wanda ya saɓa wa dokar Babban Bankin Nijeriya (CBN), ta shekarar 2007.
Hukumar EFCC ce ta gurfanar da shi, inda ta ce Amuscap ya liƙa da taka Naira 100,000 a wajen shagalin bikin, abin da ta bayyana a matsayin rashin girmamawa ga kuɗin ƙasa.
Dokar ta ce duk wanda ya liƙa ko ya taka kuɗi zai fuskanci hukuncin ɗaurin wata shida ko tara Naira 50,000 ko dukkaninsu.
A baya ma, an ɗaure wasu shahararrun mutane irin su Bobrisky da jarumar fina-finan Nollywood, Oluwadarasimi Omoseyin, bisa laifin irin wannan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp