• English
  • Business News
Saturday, November 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kotu Ta Daure Hadimin Tambuwal Kan Yada Bidiyon Da Ake Wa Matar Gwamna Liki Da Dala

by Abubakar Sulaiman
1 year ago
Tambuwal

Kotun majistare ta daya da ke Sakkwato a yau ta tura mataimaki na musamman ga Sanata Aminu Waziri Tambuwal kan yada labarai, Shafi’u Umar Tureta a gidan gyaran hali a bisa ga yada bidiyon matar Gwamna Ahmed Aliyu a yayin da ake yi mata liki da Dala.

Mai Shari’a Fatima Hassan ta daga zaman kotun kan hukuncin da za a yi kan dan shekaru 36 zuwa ranar 6 ga Satumba da za a yanke shawarar bayar da belinsa kan laifin batanci. Sai dai duk kokarin manema labarai na halartar zaman kotun ya faskara kansancewar an haramta musu shiga.

  • Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje 14,940 A Sokoto
  • Kotu Ta Ɗaure Hadimin Tambuwal Kan Yaɗa Bidiyon Da Ake Yi Wa Matar Gwamnan Sakkwato Liƙi Da Dala

Mai shigar da kara ta bayyana bayyanan a ranar 18/7/2023 cewa ya yada bidiyon matar Gwamna, Fatima Ahmed Aliyu a yayin da take bukin zagayowar ranar haihuwarta tare da cewar ta na almubbazaranci a liki da kashe kudin a yayin da al’umma ke a cikin yunwa.

Laifi na biyu da aka tuhumi shafukan shi ne sanya tsohuwar takardar kammala makarantar sakandiren Gwamna da sakamakon F9 tare da kiran sa bakauye bai iya magana da turanci ba, lamarin da dansanda mai shigar da kara Abdurrahman Mansur ya ce sun saba wa kundin dokar penal code ta jihar ta 2019 sashe na 378 da 379.

Sai dai jam’iyyar PDP a jihar ta ce ba Shafi’u ne ya dauki bidiyon da Gwamna ke turanciin ba don ba ya da damar shiga gidan gwamnati inda aka dauki bidiyon haka ma bai halarci bikin zagayowar ranar haihuwar matar gwamnan ba don haka ba inda zai same su idan ba yaran gwamnan da taimakonsa ne suka yada ba.

LABARAI MASU NASABA

Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya

Kakakin jam’iyyar, Hassan Sahabi Sanyinnawal ya bayyana mulkin kama – karya ne jaridun Sakkwato ke yi tare da kokarin cin zarafin ‘yan adawa ko ‘yan PDP, domin hakan rashin adalci ne kuma ba za su zuba ido a na nuna wa magoya bayan su ba.

A nata bangaren kungiyar kare hakkin zan’adam ta Amnesty International ta bi sahun wadanda suka soki lamarin, ta ce kama hotunan ya sabawa ‘yancinsa na dan’adam don haka ta yi Allah – wadai da kamen tare da kiran a gaggauta sakin sa.

Kungiyar ta ce maimakon kama marubucin wanda ya yada bidiyon da matar gwamna ke almubbazaranci da kudi, kamata ya yi a alakanta abin da wahala da matsalar da ake ciki ta fatara, yaran da ba su zuwa makaranta da ke gararanba kan tituna da shan wahala tsaro da ta kassara gabashin jihar

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga
Labarai

Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

November 8, 2025
Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya
Manyan Labarai

Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya

November 8, 2025
Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi
Manyan Labarai

Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi

November 8, 2025
Next Post
Wasu Barayin Shanu Da Hatsabiban ‘Yan Bindiga Sun Shiga Hannu

Wasu Barayin Shanu Da Hatsabiban ‘Yan Bindiga Sun Shiga Hannu

LABARAI MASU NASABA

Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

November 8, 2025
Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

November 8, 2025
Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko

Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko

November 8, 2025
CMG Ya Watsa Jerin Shirye-Shirye Don Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

CMG Ya Watsa Jerin Shirye-Shirye Don Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

November 8, 2025
CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

November 8, 2025
Xi Ya Yi Kiran Zurfafa Gyare-gyare Da Bude Kofa A Yayin Rangadin Aiki A Guangdong

Xi Ya Yi Kiran Zurfafa Gyare-gyare Da Bude Kofa A Yayin Rangadin Aiki A Guangdong

November 8, 2025
Ta’aziyyar Rasuwar Jarumin Kannywood, Malam Nata’ala

Ta’aziyyar Rasuwar Jarumin Kannywood, Malam Nata’ala

November 8, 2025
Kamfanoni Masu Jarin Waje Na Samun Kwarin Gwiwa Daga CIIE

Kamfanoni Masu Jarin Waje Na Samun Kwarin Gwiwa Daga CIIE

November 8, 2025
Lalacewar Tarbiyar Dalibai Mata A Makarantun Islamiyya Da Na Boko

Lalacewar Tarbiyar Dalibai Mata A Makarantun Islamiyya Da Na Boko

November 8, 2025
Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya

Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya

November 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.