A wani ci gaba da rundunar ‘yansanda a Jihar Kaduna ta gudanar, ta cafke wasu barayin shanu biyu da wasu fitattun ‘yan bindiga guda biyu, tare da dakile wani yunkurin yin garkuwa da mutane a wasu ayyuka daban-daban a jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, Mansir Hassan, ya kara da cewa ‘yansandan sun kama Aminu Saleh da Jafar Ibrahim, ‘yan kungiyar asiri ne da ke da alhakin satar shanu daga manoman da ba su ji ba ba su gani ba a yankin Kasuwa Magani da ke Kujama.
- Dan Takarar Gwamnan Katsina A NNPP Ya Ba Da Tallafin Miliyan 50 Ga ‘Yan Gudun Hijira
- CDD Ta Soki NBC Kan Cin Tarar Trust TV Da Wasu Miliyan 20
A wani labarin kuma, Hassan, a wata sanarwa da ya fitar ya ce jami’an ‘yansanda sun kuma dakile wani yunkurin yin garkuwa da su tare da kama wasu mutane uku Umar Baso, Shehu Filani, da Babangida Abdulkarim wadanda ke neman kudin fansar Naira miliyan 10 daga hannun wadanda aka sace.
Ya ci gaba da cewa rundunar ‘yan sandan ta kama wasu mutane biyu, Dahiru Liman da Sani Abdullahi Makeri da ke da hannu wajen samar da makamai da alburusai ga masu garkuwa da mutane da ke aiki a Jihohin Kaduna, Katsina da Zamfara.
A cewarsa, an samu nasarar kwato bindiga kirar AK-47 da harsashi mai tsawon millimita biyar a yayin samamen.
Kakakin rundunar ‘yansandan ya nakalto kwamishinan ‘yansandan jihar, Audu Ali Dabigi, ya yaba wa ‘yansandan bisa kokarin da suke yi, ya kuma bukaci jama’a da su sanya ido tare da kai rahoto ga ofishin ‘yansanda mafi kusa.
Ya kuma tabbatar wa mazauna jihar kan kudurin hukumar na wargaza hanyoyin sadarwar masu aikata laifuka da kuma tabbatar da tsaro da jin dadin dukkan ‘yan kasa a fadin jihar.
Sanarwar ta ce, “A ranar 22 ga watan Agusta, 2024, jami’an ‘yansanda sun yi nasarar kai samame a wata maboyar da wasu ‘yan kungiyar asiri masu satar shanu ke amfani da ita a unguwar Kasuwa Magani da ke Kujama, Kaduna. An kama wasu mutane biyu, Aminu Saleh mai shekaru 25 da Jafar Ibrahim mai shekaru 24, kuma sun amsa laifinsu.
“A wani lamari na daban, jami’an ‘yansanda sun dakile yunkurin sace mutane tare da kama wasu mutane uku Umar Baso, Shehu Filani, da Babangida Abdulkarim wadanda ke neman kudin fansa Naira miliyan 10m.
“Bugu da kari, a ranar 24 ga Agusta, 2024, jami’an tsaro sun kama wasu mutane biyu, Dahiru Liman mai shekaru 47 da Sani Abdullahi Makeri mai shekaru 45, wadanda ke da hannu wajen samar da makamai da alburusai ga masu garkuwa da mutane da ke aiki a jihohin Kaduna, Katsina da Zamfara. An samu nasarar kwato bindigu kirar AK-47 guda daya da harsashi mai girman millimita 9 a yayin samamen.
“Kwamishanan ‘yansandan Jihar Kaduna, Audu Ali Dabigi, ya yaba wa ‘yansandan bisa kokarin da suke yi, ya kuma bukaci jama’a da su sanya ido tare da bayar da rahoton duk wani abu da ake zargin su da aikatawa tare da tabbatar wa mazauna yankin kudurin rundunar na wargaza hanyoyin sadarwa da kuma tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ga dukkan ‘yan kasa.