Wata Babbar Kotun Jihar Bayelsa da ke zamanta a Yenagoa ta yanke wa wani mutum mai suna Baridapsi Needam mai shekaru 41 hukuncin daurin shekara 14 a gidan yari bisa samunsa da laifin yi wa ‘yarsa ciki ta hanyar fyade.
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya, NAN, ya ruwaito a daidai lokacin da ake shari’ar an bayyana cewa yarinyar da aka yi wa cikin ta haifi ‘ya mace.
- Binciken Ganduje: Kotu Ta Bai Wa Alkalan Kano Sa’o’i 48 Su Yi Murabus
- Kotu Ta Rushe Dokar Da Ta Tsige Aminu Ado Bayero A Matsayin Sarkin Kano
Kwamishinan Shari’a na Jihar Bayelsa, kuma Babban Lauyan Gwamnati, Briyal Dambo, a kara mai lamba YHC/14C/2022, ya tuhumi wanda ake zargin da laifin aikata laifin fyade da ya saba wa sashe na 1 (1) na dokar cin zarafin jama’a ta Jihar Bayelsa ta 2021.
Pere Amanda Egbuson, lauya mai shigar da kara na ma’aikatar shari’a ta Bayelsa, ya shaida wa kotun cewa bincike ya nuna cewa wanda ake zargin Needam ya fara cin zarafin ‘yarsa tun tana ‘yar shekara bakwai.
Egbuson ya ce Needam ya lalata ‘yar ne ta hanyar sanya yatsunsa a cikin al’aurarta kafin ya san ta ‘ya mace a shekarar 2020 har zuwa lokacin da ta samu ciki.
Mai shari’a D.E. Adokeme, yayin da yake yanke hukunci, ya bayyana cewa masu gabatar da kara sun gabatar da sahihiyar shaida tare da yin bincike kan sakamakon DNA, wanda ya nuna cewa kashi 99.99 cikin 100 tabbataccen rahoton cewa wanda aka yankewa hukuncin shi ne mahaifin yaron.
Kotun ta yanke hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari, inda mai gabatar da kara ya tabbatar da cewa Needam ta aikata laifin fyade.
Da yake magana bayan yanke hukuncin, Egbuson, jagoran masu shigar da kara, ya lura cewa hukuncin zai zama izna ga sauran masu aikata irin wadannan abubuwa na wuce tunanin dan dan’adam.
Ta gode wa babban mai shari’a kuma kwamishinan shari’a, Biriyai Dambo, bisa goyon bayan da ya bayar wajen ganin an gudanar da binciken DNA domin taimakawa masu gabatar da kara.
Da take mayar da martani kan wannan ci gaban, wata fitacciyar mai fafutukar yaki da cin zarafin mata, kuma wacce ta kafa gidauniyar Do Foundation, Dakta Dise Ogbise-Goddy Harry, ta yaba wa kotun bisa tabbatar da adalci.
“Gwamnatin Jihar Ta Hannun Ma’aikatar Shari’a, Ma’aikatar Harkokin Mata, Harkokin Yara da Ci Gaban jama’a da kuma kungiyar daidaita jinsi ta Jihar Bayelsa sun yi aiki mai kyau wajen ba wa wacce abin ya shafa kariya da kuma jaririyar.
Idan dai ba a manta ba Kungiyar Kare Hakkin Mata ta Jihar Bayelsa, ‘Gender Response Initiatibe Team’ (GRIT) ta mika Needman ga ‘yansanda, bayan da wani makwabcin da ya gano cewa shi ke da alhakin yi wa ‘yarsa ciki a shekarar 2022.