Alkalin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, Mai shari’a James Omotosho, ya dawo da Philip Shaibu a matsayin mataimakin gwamnan Jihar Edo watanni bayan sauke shi daga mukamin.
A hukuncin da ya yanke a ranar Laraba, Mai shari’a Omotoso, ya ce tsige shi da Majalisar Dokokin Jihar Edo ta yi ya saba wa kundin tsarin mulkin Nijeriya.
- Kwalara Ta Hallaka Mutane 103, Mutane 3000 Sun Kamu A Nijeriya
- ‘Yan Nijeriya 15 Ne Suka Rasu A Hajjin Bana – NAHCON
Bayan dawo da Shaibu, kotun ta kuma bayar da umarnin a biya shi albashi da alawus-alawus tun daga lokacin da aka tsige shi daga mukamin mataimakin gwamnan jihar.
A halin da ake ciki, majalisar dokokin Jihar Edo, ta daukaka kara kan hukuncin da babbar kotun ta yanke.