Kotun tarayya da ke zamanta a jihar Kano, ta ki amincewa da bukatar mayar da shari’ar Sheikh Abduljabbar Kabara zuwa babban birnin tarayya, Abuja.
Abduljabbar dai ya bukaci kotun da ta mayar da shari’ar tasa zuwa wata kotun a Abuja saboda zargin da yake na cewar kotun Kano ba za ta yi masa adalci ba.
- Barazanar ‘Yan Bindiga: Gwamnatin Nasarawa Ta Rufe Duk Makarantun Jihar
- Rashin Tsaro: NYSC Ta Nemi Karin Sojoji A Sansanonin Masu Yi Wa Kasa Hidima
A yayin zaman kotun na yau Alhamis, wanda ya gudana karkashin mai shari’a Abdullahi Liman, lauyan Abduljabbar Nasir Kabara, Barista Dalhatu Shehu Usman, ya zargi alkalin kotun tarayyar na Kano da ganawa da kwamsihinan shari’a na Kano, Barista Musa Lawan a safiyar yau gabanin zaman kotun.
Wanda ya ce bisa ka’ida bai kamata a ce alkalin ya yi hakan ba, wanda kuma hakan yasa Sheikh Kabara ya karaya da cewar ba zai samu adalci a kotun ba.
Sai dai a wani martani da lauya gwamnati, Barista Dahiru Muhammad, ya kalubalanci wannan batu.
Ya sanar da kotun cewar tun karfe 9 na safiyar yau, masu gabatar da karar suka ba shi kwafin wata sabuwar karar da suka shigar a Abuja na zargin take hakkinsa na dan adam, bayan batun na gaban alkalin wata kotu ta daban.
Daga nan ne mai shari’a Abdullahi Liman, ya ce ba zai rufe shari’ar ba, sannan a shari’ance babu inda aka ce bangare daya da ake shari’a da shi zai ce lallai shi ga kotun da yake bukata da ta saurari wata shari’ar.
Sannan ya umurci lauyan Abduljabbar da ya rubuto zargin da yake yi kan zuwan Kwamishinan shari’a na jihar Kano wajensa, tare da tabbatar da abin da suka tattauna na da alaka da shari’ar ta Abduljababr din ya shigar gabansa.
LEADERSHIP ta ruwaito a ranar 21 ga watan Yulin da muke ciki ne Shiekh Abduljabbar, ya garzaya kotun tarayyar da ke Kano, da bukatar a mayar da shari’ar da ake yi masa ta zargin batancin ga Annabi S.A.W zuwa ga wani alkalin daban.
Ya yi hakan ne saboda zargin cewar gwamantin Kano da Babbar Kotun Musulunci ta Kofar Kudu na take masa hakkinsa a matsayinsa na dan Adam.