Mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja, ya yi watsi da karar da Abdulrasheed Maina ya shigar a kan ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, da kuma babban jami’in gidan gyaran hali na Nijeriya, Haliru Nababa, bisa zargin tauye masa hakki.
Da yake yanke hukunci, Mai shari’a Ekwo, ya ce Maina bai bayar da wata kwakkwarar hujjar da ke nuna cewa ministan da CG sun tauye masa wani hakki nasa ba kamar yadda doka ta tanadar a lokacin da yake tsare.
- Sin Za Ta Ci Gaba Da Hada Hannu Da Mambobin G20 Game Da Tsarin Tattalin Arziki Na Zamani
- 2023: Indiya Za Ta Rage Kudin Zuwa Aikin Hajji
Alkalin ya dauki bukatar Maina a matsayin yaudara da kuma kokarin raina ma’anar hukuncin aikata laifi da kuma taimaka wa Maina koma kam turba.
Mai shari’a Ekwo ya yi watsi da bukatarsa saboda rashin cancanta.
Maina, wanda tsohon Shugaban Hukumar Fansho ne, ya shigar da kara a ranar 17 ga Oktoba, inda ya gabatar da wani kuduri na neman a kula da lafiyarsa cikin gaggawa saboda yana fama da wata cuta mai barazana ga rayuwa.
Tsohon shugaban hukumar fanshon ya roki kotun da ta ba shi umarnin wucin gadi da ya umarci ministan da CG ta hannun ma’aikatansu ko jami’ansu da su kai shi wani babban asibiti domin jinyar cututtukan da ke barazana ga rayuwarsa har zuwa lokacin da za a yanke hukunci.
Yanzu haka Maina yana zaman gidan yari na shekara takwas a gidan yari na Kuje da ke Abuja bisa samunsa da laifin almundahanar kudin fansho har Naira biliyan biyu.