Mai shari’a Obiora Egwatu, na babbar kotun tarayya da ke Abuja, ya soke zaben fidda gwani na jam’iyyar APC da ya tsayar da Sanata Emmanuel Bwacha a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar a zaben 2023 mai zuwa.
Da yake yanke hukuncin, Mai shari’a Egwuatu ya bayyana cewa bisa ga shaidun da dukkan bangarorin da abin ya shafa suka gabatar a gabansa, zaben fidda gwanin da jam’iyyar APC ta gudanar a ranar 26 ga watan Mayun wannan shekara inda jam’iyyar ta bayyana Bwacha na APC a Taraba ta Kudu a matsayin dan takararta na gwamna a zaben 2023 ba halastace ba ne.
- Sufeton ‘Yansanda Ya Ba Da Umarnin Tsaurara Tsaro A Hanyar Legas-Ibadan
- Sabon Shugaban PDP Na Katsina Ya Nemi Haɗin Kai A Tsakanin ‘Ya’yan Jam’iyyar
Sanata mai wakiltar Taraba ta tsakiya, Yusuf Yusuf ne ya garzaya kotu kan zaben.
Wata babbar kotun tarayya da ke Jalingo ta kori Bwacha a watan jiya, Babban birnin Jihar Taraba, a wata shari’a ta daban da wani dan takarar gwamna, David Kente ya shigar.
A hukuncin da suka yanke, kotunan biyu sun bukaci shugabannin jam’iyyar APC da su gudanar da sabon zaben fidda gwani na gwamna a Taraba.