Wata kotun majistare da ke Kano a jiya Juma’a, ta bayar da umarnin a yi wa wani matashin tela mai shekaru 20, Abubakar Sani bulala 12 bayan samunsa yana kwankwadar kodin.
Sani, wanda ke zaune a unguwar Fagge a jihar Kano, an yanke masa hukuncin ne bisa laifin takurawa al’umma da kuma mallakar kayan mayen.
- EFCC Ta Yi Kamen Masu Canjin Da Ke Boye Dala A Abuja
- Sayen Kuri’u Na Kara Dagula Dimokuradiyyar Nijeriya — Sanusi II
Alkalin kotun, Farouk Ibrahim Umar, ya kuma yanke masa hukuncin zaman gidan yari na tsawon wata biyu ba tare da zabin biyan tara ba.
Tun da fari, lauyan masu shigar da kara, Aminu Dandago, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne a ranar 16 ga watan Yuni 2022, a unguwar Fagge.
Ya ce a wannan ranar, da misalin karfe 9 na dare, tawagar ‘yan sandan da ke aiki a ofishin ‘yan sanda na Fagge, ta kama shi a lokacin da yake sintiri a cikin unguwa.
Rundunar ‘yan sandan ta ce an kama Sani ne da kwalba daya ta maganin kodin da ake zargin yana cikin maye.