Kotun babban birnin tarayya (FCT) ta bayar da belin tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, kan Naira miliyan 500, tare kawo shaidu shaidu biyu da za su kawo irin wannan adadi. A ranar 10 ga Disamba, Mai Shari’a Maryann Anenih ta ki amincewa da buƙatar belin da aka gabatar daga lauyoyin tsohon gwamnan a baya, tana cewa an shigar da bukatar ba bisa ƙa’ida ba.
Tsohon gwamnan na fuskantar tuhumar aikata laifin safarar kuɗaɗe da suka kai Naira biliyan 110 tare da da haɗin bakin wasu mutane biyu. Sai dai ya musanta aikata laifukan da ake tuhumarshi da su a gaban hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziki zagon ƙasa zagon ƙasa (EFCC).
A yayin da ake ci gaba da shari’ar, lauyan Yahaya Bello, Joseph Daudu, SAN, ya shaida wa kotu cewa an gabatar da ƙarin wasu tuhumar don amsa hujjojin lauyoyin masu gabatar da ƙara, amma an nemi kotu ta janye wannan karin takardun domin kaucewa rikici.
Kotun ta amince da wannan buƙata kuma ta janye ƙarin tuhumar. An kuma tattauna tsakanin lauyoyin da aka kammala a cikin lokaci, wanda ya kai ga buƙatar kotu ta ba da belin tsohon gwamnan.