Babban Kotun Tarayya da ke zamanza a Birnin Kebbi a karkashin Jagorancin mai shari’a Baba Gana Ashigar ya tabbatar da Alhaji Haruna Saidu Dandiyo a matsayin halatacin dan takarar kujerar Sanatan Kebbi ta tsakiya a karkashin jam’iyyar PDP a jihar Kebbi.
Alhaji Haruna Saidu, wanda ya shigar da karar ya kai karar Sanata Muhammad Adamu Aliero, PDP da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) domin ya gudanar da sabon zaben fidda gwani na mazabar Kebbi ta tsakiya, alhali bai mutu kuma ba bisa ya janye daga takarar ba.
Ya kuma kai karar su kan sauya sunansa da sunan Sanata Muhammadu Adamu Aliero, wanda ya ce yana APC a lokacin da aka gudanar da zaben fidda gwani na farko, sabanin dokokin zaben 2022 da kundin tsarin mulkin Jam’iyyar PDP.
Yayin da yake yanke hukunci a kan karar, Mai Shari’a Baba Gana Ashigar ya yanke hukuncin
Mai shari’a Asghigar, yayin da yake gabatar da hukuncin nasa kan batutuwan da suka shafi gaba daya, ya lura cewa, ko shakka babu, a lokacin da aka gudanar da zaben fidda gwani na farko na mazabar Kebbi ta tsakiya a jam’iyyar PDP, wanda ake kara na 1 yana cikin jam’iyyar mai mulki watau APC.
Ya kuma kara da cewa, bisa ga hujojin da aka gabatar a gaban kotun, wanda ya shigar da karar ya halarci zaben fidda gwani na mazabar Kebbi ta tsakiya a zaben fidda gwani na farko, inda aka zabe shi, dan takarar Sanata na jam’iyyar PDP ya samu nasarar lashe zaben da kuri’u mafi girma yayin da wanda ake kara na 1 yana a jam’iyyar APC mai mulki a yanzu. Saboda haka, kotu ta gamsu da duk hujoji da kuma rokon da mai kara,” in ji shi.
A nasa martani, Lauyan mai kara, Sule O.Usman (SAN), wanda ya yaba wa Alkalin da ya gabatar da wannan hukuncin wanda ya baiwa wanda yake tsayawa damar samun nasara a Shari’ar.
A cewarsa, “Mun yi murna saboda mun tunkari Kotun da ta share Mana hawaye a fuskarmu, inda kotu ta tabbatar da Saidu Haruna Dandiyo a matsayin dan takarar kujerar Sanatan Kebbi ta tsakiya a PDP.
Lauyan wanda ake kara na daya, Barista Aminu Hassan wanda ya tsayawa I K. Sanusi SAN, wanda shi ma ya yabawa mai shari’a Baba Gana Ashigar bisa hukuncin da aka yanke kuma ya yaba da aikin da ya yi masa amma ya shaida wa manema labarai cewa, Sanata Muhammad Adamu Aliero zai daukaka kara kan hukuncin.
A nasa martani, Lauyan Hukumar INEC, Barista Ahmad Bello Mahamud ya ce sun koyi darasi da yawa a cikin hukuncin kuma ya yaba wa Mai Shari’a Ashigar bisa yanke hukunci da yayi.