Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke zargin cin amanar kasa da ake yi wa yaran da aka kama zanga-zangar #EndBadGovernance guda 150.
An soke tuhumar ne bayan Antoni Janar na Tarayya, Prince Lateef Fagbemi, ya janye karar da ake musu a madadin gwamnatin tarayya.
- An Bude Baje Kolin CIIE Karo Na 7 A Birnin Shanghai
- An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno
Alkalin kotun, Mai Shari’a Obiora Egwuatu, ya amince da bukatar janye karar tare da bayar da umarnin sakin yaran da aka tsare.
Yawancin wadanda ake tuhuma matasa ne, kuma doka ta hana irin wannan tuhuma a kansu.
Shugaba Bola Tinubu ne ya umarci Antoni Janar ya dakatar da shari’ar da ake yi wa yaran tare da bayar da umarnin sakin su a ranar Litinin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp