A wani rahoto da jaridar daily nigeria ta fitar, ta bayyana cewa, wata babbar kotu a jihar Kano ta soke umarnin kwace wani fili mallakar kamfanin ‘Tiamin Multi Services Global Limited’ tare da bayar da umarnin biyan diyyar Naira biliyan 2.6 ga kamfanin.
Filin, wanda ke kan titin kotu rod, Gyadi-gyadi, a karamar hukumar Tarauni, gwamnatin tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje ce ta kwace tare da rusa ginin da ake kan ginawa a lokacin da aka kwace kuma aka rusa.
- Boko Haram: Majalisar Dattijai Ta Amince Da Kafa Sansanin Sojoji A Hong Ta Jihar Adamawa
- Za A Gudanar Da Baje Kolin Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Karo Na 4 A Birnin Changsha Dake Lardin Hunan
Don haka, kamfanin ya garzaya kotu, inda ya nemi a biya shi diyyar kwacewa da rushe masa gini ba bisa ka’ida ba, wanda ake kyautata zaton Asibitin zamani ake ginawa a wurin.
A wani hukunci da ya yanke a ranar Laraba, alkalin kotun, Ibrahim Karaye, ya ce soke hakkin wanda ya shigar da kara ya sabawa ka’ida, ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa, kuma hukuncin ba shi da tushe balle makama.
Karaye ya ci gaba da cewa, sanarwar kwace shaidar mallakar filin a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan Satumba 3, 2021, daga ofishin kula da filaye na jihar Kano, an yi ta ne ba tare da an yi shari’a ta adalci ba, wanda hakan ya saba wa tanadin dokar amfani da filaye.
Alkalin ya ci gaba da bayyana cewa, takardar shaidar mallakar fili ta asali mai lamba LKN/COM/2017/116 [wacce aka sake shedawa a matsayin LPKN 1188], MLKN01622, da MLKN01837 – suna nan da inganci kuma sahihai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp