Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Fatakwal, a ranar Alhamis, ta kori dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a Jihar Ribas, Tonye Cole, kan samunsa da katin dan kasa na kasashe daban-daban.
An rawaito cewar Tonye Cole dan asalin Birtaniya ne.
- Kotun Daukaka Kara Ta Dawo Wa Da Aishatu Binani Takararta Ta Gwamna A Adamawa
- Gasar Kofin Duniya: Kasar Japan Ta Lallasa Germany Da Ci 2 Da 1
Kotun ta kuma ce APC ba ta bi dokar zabe da ta kawo Cole a matsayin dan takarar jam’iyyar ba.
Jam’iyyar PDP a Jihar Ribas ta garzaya kotu da ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta da kada ta amince da Tonye Cole a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar APC bisa zargin zama dan kasa guda biyu kuma wakilan jam’iyyar ba su kawo shi bisa bi ka’ida.
An umarci INEC da ta cire sunan Tonye Cole daga cikin sunayen wadanda suka cancanci tsayawa takarar gwamna a zaben 2023.
Hukuncin kotun dai ya sabawa hukuncin da ta yanke tun farko a kan karar da jam’iyyar APC ta shigar da jam’iyyar PDP da kuma dan takararta na gwamna Siminialaye Fubara.
A cikin karar, mai shari’a Obile ya yanke hukuncin cewa babu wata jam’iyya da ke da hurumin yin katsalandan cikin harkokin cikin gida na wasu jam’iyyun siyasa sannan kuma ya ce kotu ba ta da hurumin sauraren karar.
Da yake zantawa da manema labarai a wajen kotun, lauyoyin jam’iyyar PDP, Dike Udenna, ya bayyana farin cikinsa kan hukuncin da ya ce APC ba ta da dan takarar gwamna a zaben 2023.
A nasa bangaren, lauyan jam’iyyar APC, Collins Dike ya ce APC za ta kalubalanci hukuncin a kotun daukaka kara.
Ya ce kundin tsarin mulkin Nijeriya ya ba shi damar tsayawa takarar gwamna bayan shi haifaffen Najeriya ne.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp