Wata kotun Majistire da ke Ilorin ta umarci a tsare wani dan kasuwa mai shekara 40 a duniya, Usman Baba a gidan gyara halinka bisa zarginsa da yin amfani da sarka wajen daure kafafun wata mai suna Misis Aishat Ibrahim na tsawon mako biyu.
Rahoton bayanan farko-farko na ‘yan sanda (FIR) ya ce wanda ake zargin ya aikata danyen aikin ne tare da matarsa ga wanda suka dauren bisa zargin wai ita Mayya ce.
- Ma’aikata 2 Sun Shiga Hannu Kan Zargin Sace Tiraktoci 9 A Nasarawa
- Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kano Ta Ceto Mutum 79 A Watan Yuli
Rahoton na ‘yan sanda ya kara da cewa Baba da matarsa wacce ta arce (ake nema) sun tursasa ahlin wacce suka dauren da cewa sai sun basu naira N100,000 a matsayin kudin fansa kafin su saketa.
Dan sanda mai shigar da kara, Zacchaeus Folorunsho, ya roki kotun ta tsare wanda ake zargi.
Magistrate Ibrahim Dasuki, ya amince da rokon masu kara tare da dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 22 ga watan Agustan 2022.