Wata babbar kotu da ke Jos a Jihar Filato, ta bayar da umarnin tsare wata matar aure, Nneamaka Nwachuku, bisa zargin laifin azabtar da ‘yar aikinta mai shekaru 11, Margret Joshua wadda ta mutu har lahira.
Alkalin kotun, B. Bassi, wanda ya jagoranci shari’ar, ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare wadda ake tuhumar a ranar Laraba.
An ce matar ta gallaza mata azaba wanda hakan ya sa ta mutu har lahira a ranar 11 ga watan Nuwamba.
‘Yansandan sun tuhume ta da laifuka guda uku na kisan kai, azabtarwa da kuma haifar da rauni.
Rundunar ‘yansandan ta ce Mista Nwachukwu, da ke karamar hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato, ta yi amfani da man gyada mai zafi ta zuba wa ‘yar aikin a sassan jiki.
‘Yansanda sun ce “ta ci gaba da gana mata azaba har sai da ta kai ga mutuwarta.”
Kotun ta dage ci gaba da sauraren karar zuwa ranar 19 ga watan Janairun 2023, domin masu gabatar da kara su tabbatar da karar.