Kotun Shari’ar Musulunci da ke Goron Dutse a Kano ta tura wani magidanci Auwalu Mai Yashi Kabara zuwa gidan yari.
Wani mai suna Alhaji Sabo Ado Kurawa ne ya yi kararsa a Kotun bisa zargin ya ci masa mutunci tare da barazana da rayuwarsa zargin da ya musanta.
- Kotu Ta Bukaci Masu Kalubalantar Nasarar Tinubu Su Biya Miliyan 10 Kowannensu
- Majalisa Ta 10: Gwamnoni 25 Sun Mara Wa Akpabio Da Barau Baya
Mai Yashi ya ce tun da farko Babban Malamin nan Sheikh Qariballah Nasiru Kabara ne ya yi ƙorafi a ofishin ƴan sanda na Mandawari bisa zargin Auwaulun ya ki ya daina sayar da yashi a kofar gidansu da suke yin Zikiri.
Daga nan ne jami’an ‘yansandan suka kama shi tare da tsare shi.
Auwalu Mai Yashi ya shaida wa Kotu cewa bai san Alhaji Sabo Kurawa ba sai a ofishin ‘yansanda na Mandawari, inda a nan ne ya zo a matsayin wakilin Khalifa Qariballahi.
Kuma har suka yi sa’insa da shi a ofishin Æ´an sandan, amma ga mamaki an kai shi Kotu ba bisa zargin sayar da Yashi ba.
Yayin zaman Kotun na yau mai shari’a Malam Salisu Ƙoki ya umarci a kai Auwalu Mai Yashi zuwa Kurkuku har zuwa ranar 27 ga watan Yunin da muke ciki.