Wata babbar kotun jihar Legas da ke zamanta a dandalin Tafawa Balewa, a Igbosere, ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga mataimakin Sufeton ‘yansanda (ASP), Drambi Vandi da aka dakatar, bisa laifin kashe wata lauya, Omobolanle Raheem, mazauniyar Legas.
Mai Shari’a Ibironke Harrison ne ya yanke wa ASP Drambi hukuncin kisan sakamakon harbe lauyar mai juna biyu.
A ranar 16 ga watan Janairun 2023, an gurfanar da Vandi a gaban kotu bisa laifin harbe wata lauya mai shekaru 41 a shingen binciken gada ta Ajah a ranar 25 ga Disamba, 2022 jim kadan bayan dawowa daga coci don murna da bikin ranar Kirismeti.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp