Wata babbar kotu a Jihar Ekiti, ta yanke hukuncin kisa ga wasu mutum biyu bisa kama su da laifin fashi da makami.
Baya ga wannan, kotun ta kuma daure mutanen a gidan yari na tsawon shekara bakwai bisa kama su da laifin fyade da tserewa daga magarkama a gidan yarin Ado Ekiti a ranar 1 ga watan Disamban 2014.
- Buhari Ya Halarci Wajen Kaddamar Da Hako Man Fetur A Bauchi
- Mutum 11 Sun Mutu Bayan Cin Abinci Mai Guba A Benuwai
Wadanda aka yanke wa hukuncin da farko dai an gurfanar da su a gaban mai Shari’a Monisola Abodunde a ranar 13 ga watan Janairun 2017 bisa zargin aikata laifuka.
A tuhumar da aka musu na cewa, a ranar 14 ga watan July na 2915 a yankin Oketa da ke Iluomoba Ekiti a karamar hukumar Gbonyin da ke Jihar Ekiti, sun aikata laifin fashi da makami kan Lucas Agboola da Oladele Oseyemi gami da Adeyemi Comfort dukka da suke layin Araromi, a garin Aisegba Ekiti, dauke da bindiga da adduna.
Sannan wadanda ake karar sun yi fyade ga wata mata dukka a wannan ranar, sannan suka gudu daga gidan yari a Ado Ekiti a ranar 1 ga watan Disamban 2914.
Mai shigar da kara, Mr Ilesanmi Adelusi ya kira shaidun gani da ido biyar, bindiga guda, wayoyin salula goma, tocila mai amfani da caji, Batirin waya guda hudu, kudi naira 21,060, katina waya da bayanan wadanda Ake zargi domin tabbatar wa kotu da tuhume-tuhumen da suke musu.