An yanke wa sanannen wanda ake zargi da laifin garkuwa da mutane Hamisu Bala, wanda aka fi sani da Wadume, hukuncin daurin shekara bakwai a gidan yari.
Mai shari’a Binta Nyako, ta samu Wadume da laifin tserewa daga hannun hukuma da kuma yin mu’amala da muggan makamai ba bisa ka’ida ba.
- Dabi’ar Yawan Roko A Tsakanin Yara
- Yang Jiechi Ya Halarci Bikin Bude Baje Kolin Kasa Da Kasa Na Hanyar Siliki Karo Na Shida Tare Da Gabatar Da Jawabi
Mai shari’a Nyako ta kuma yanke wa Rayyanu Abdul hukuncin daurin shekara uku saboda ya ajiye Wadume a gidansa da ke Kano bayan Wadume ya tsere daga hannun ‘yan sanda a Ibi.
Alkalin kotun ta soke tuhuma ta daga, inda ake tuhumar Wadume da laifin yin garkuwa da Usman Garba wanda aka fi sani da Mayo da kuma karbar Naira miliyan 106 kafin a sake shi.
Mai shari’a Nyako, ta yanke hukuncin ne a ranar 22 ga watan Yulin bana.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp