Wata babbar kotu ta daya da ke Birnin Kebbi, ta yanke wa wani dan kasar Jamhuriyar Nijar, Sulieman Idris, hukuncin kisa ta hanyar rataya , bisa samunsa da laifin kisan matar aure da’yar ta ‘yar shekara hudu da haihuwa a duniya.
Lauyoyin jihar sun gurfanar da Suleiman Idris a gaban kuliya tare da tuhumar shi da laifuka biyu na kisan kai wanda hukuncin kisa ne a karkashin sashe na 191 (a) da (b) na dokar Penal Code na jihar Kebbi, 2021.
Da yake yanke hukunci, Mai shari’a kuma Babbar jojin Jihar Sulieman Muhammad -Ambursa, ya ce masu gabatar da kara sun yi nasarar tabbatar da dukkan hujojin su da babu shakka a gaban kotu, inji kotun”
“A bisa la’akari da nauyi da shaidun da lauyoyin masu gabatar da kara su gabatar a gaban kotu, wadanda suka nuna tabbacin aikata laifin da ake tuhumar Sulieman Idris a gaban kotun sun tabbata, inji kotun”.
“ Haka Kuma bisa ga doka, tuhume-tuhume biyu na aikata laifin kisan kai da ke da hukuncin kisa a karkashin sashe na 191 (a) da (b) a karkashin dokar Penal Code, 2021 an tabbatar da su kuma wanda ake tuhumar ya nuna cewa ya aikata laifin da ake tuhumar su da aikatawa a gaban wannan kotu.
“A bisa hujojin da suka nuna aikata laifin kisa da aka tuhumi Sulieman Idris, kotu ta yanke maka hukuncin kisa bisa laifin da kotu ta kama ka da shi. Don haka kotu ta yanke maka hukuncin kisa ta hanyar rataya har sai ya mutu, inji kotu”.
“Game da roƙon neman adalci tare da jinƙai ga waɗanda ake tuhuma da lauyan nasa ya yi, kan yanke masa hukunci.
Bugu da kari, kotu ta ce” kai Sulieman Idris, an yanke maka hukuncin kisa ta hanyar rataya, kuma a rataye ka da wuya har ka mutu,inji kotun”.
Tun da farko, mai gabatar da kara, Barista Zainab muhammad- Jabbo, ta shaida wa kotun cewa wanda ake kara ya aikata laifin da ya kashe matar har lahira tare da buga kan karamar yarinyar a kan tayal dakin mahaifiyar, wanda ya kai ga mutuwarta a ranar 11 ga Afrilu.
Ta ce bangaren da aka aikata laifukan a cikinsa ba shi da hurumi, don haka ta roki kotu da ta hukunta wadanda ake tuhuma kamar yadda yake kunshe a sashin.
A nasa jawabin, Lauyan mai kare wanda ake tuhumar, Barista Alhassan salihu-Muhammad, ya roki kotun da ta yi adalci da rahama wajen yanke wa wanda ake tuhuma hukuncin daurin rai da rai, kamar yadda ya nuna nadamar matakin da ya dauka.
Mijin marigayin, Malam Akilu Aliyu, wanda ya bayyana jin dadinsa da hukuncin, ya roki gwamnatin jihar da ta gaggauta zartar da hukuncin.