Babbar kotun Jihar Sakkwato, ta yi watsi da ƙarar da ɓangaren tsohon gwamnan jihar, Attahiru Bafarawa, suka shigar, inda suke ƙalubalantar sahihancin zaɓen shugabannin jam’iyyar PDP na jihar.
A hukuncin da ya yanke, mai shari’a Kabiru Ahmad ya bayyana cewa zaɓen shugabannin jam’iyya lamari ne da ya shafi cikin gida na jam’iyyar, don haka waɗanda suka shigar da ƙarar ba su da hurumin yin hakan.
- Hare-haren ‘Yan Bindiga Sun Ragu A Watan Disamban 2024, Amma Har Yanzu Ana Fuskantar Barazana – Rahoto
- Mahalarta Ɗaurin Aure 19 Daga Kano Sun Rasu A Hatsarin Mota A Filato
Ya ce kotu ba ta da zaɓi face ta kori ƙarar.
Rikici ya kunno kai a PDP tun bayan zaɓen 2023, musamman a ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamna Aminu Waziri Tambuwal.
Rikicin ya ƙara tsananta a lokacin zaɓen shugabannin mazaɓu na jam’iyyar a 2024, inda ɓangaren da ke goyon bayan Attahiru Bafarawa suka yi zargin rashin adalci.
Ɓangaren Bafarawa sun kai ƙarar gaban kotu, suna neman a soke zaɓen shugabannin mazaɓu, suna zargin cewa an hana wasu ’ya’yan jam’iyyar damar sayen fom ɗin tsayawa takara domin a sharewa wasu hanya.
Lauyansu, Ibrahim Abdullah, ya ce hakan ya saɓa wa dokar zaɓe ta 2022 da kuma kundin tsarin mulkin ƙasa.
Sai dai, ɓangaren PDP da Bello Goronyo ke jagoranta sun musanta zargin.
Lauyan jam’iyyar, A.Y. Abubakar, ya shaida wa kotu cewa waɗanda suka kai ƙarar ba su da rajistar jam’iyyar, kuma lamuran da suka shafi zaɓen shugabannin jam’iyya ya kamata a warware su a cikin gida, ba gaban kotu ba.
Bayan sauraron ɓangarorin biyu, kotu ta yanke hukuncin korar ƙarar, tana mai cewa ba ta da hurumin shiga cikin rikicin cikin gida na jam’iyyar.