Kotun Tarayya da ke Abuja ta ƙi amincewa da buƙatar Ministan ƙirƙire-ƙirƙire, Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji, wanda ya nemi hana Jami’ar Nsukka (UNN) fitar da bayanan karatunsa.
Nnaji ya shigar da ƙara kan Ministan Ilimi, da Hukumar NUC, da jami’an jami’ar — ciki har da Shugaban Jami’ar, da Magatakarda, da Majalisar Jami’ar, yana neman kotu ta hana su fitar da bayanan karatunsa. Amma Alƙaliyar Hauwa Yilwa ta ƙi amincewa da wannan roƙo, tana mai cewa buƙatar ba ta da hujjar da ta isa don bayar da kariya ga ƙin bayyanawar.
- Kotu Ta Yi Watsi Da Ƙarar Da Aka Shigar Da Tinubu Kan Sanya Dokar Ta-Ɓaci A Ribas
- Kotu Ta Dakatar Da PENGASSAN, NNPCL Kan Katse Wa Matatar Ɗangote Ɗanyen Mai Da Iskar Gas
Ministan ya nemi kotu ta hana jami’ar ta taɓa bayanansa da kuma ta tilasta musu su fitar masa da takardun karatu, amma kotu ta amince da wasu buƙatu na farko kawai, ta ƙi amsa roƙon da ya shafi hana jami’ar fitar da bayanai.
Lamarin ya samo asali ne daga wasiƙar da Shugaban Jami’ar Nsukka, Farfesa Simon Ortuanya, ya aikawa da jaridar Premium Times a ranar 2 ga Oktoba, 2025, inda jami’ar ta nesanta kanta daga takardar shaidar Nnaji, tana cewa bai kammala karatunsa ba.
A cikin takardunsa na kotu, Nnaji ya amince cewa bai karɓi takardar shaidar kammala karatu daga jami’ar ba, abin da ya saɓa da bayanan da ya gabatar wa majalisar dattijai a shekarar 2023, inda ya bayyana kansa a matsayin mai digiri na kimiyyar Microbiology/Biochemistry daga UNN.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp