Kotun Ƙoli ta tabbatar Da Sanata Monday Okpebholo a matsayin sahihin Gwamnan Jihar Edo.
Kotun ta yanke hukuncinta ne a ranar Alhamis, inda ta kawo ƙarshen shari’ar da aka dinga yi bayan zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 21 ga watan Satumban 2024.
- ‘Yansanda Sun Kama Mutum 22 Kan Zargin Kisan ‘Yan Ɗaurin Aure A Filato
- Buhari Ba Mutum Ne Mai Son Abun Duniya Ba – Gowon
Kwamitin alƙalai biyar ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Mohammed Garba, ya ce ƙarar da Asue Ighodalo na jam’iyyar PDP ya shigar ba ta da ƙarfi, don haka kotun ta yi watsi da ita.
Mai Shari’a Garba, ya bayyana cewa PDP da ɗan takararta ba su kawo wata hujja mai ƙarfi da za ta nuna cewa Okpebholo bai lashe zaɓen bisa ƙa’ida ba.
Haka kuma ba su nuna yadda hukuncin kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe da na kotun ɗaukaka ƙara ya saɓa doka ba.
“Mun yi watsi da ƙarar saboda babu ingantacciyar hujja a cikinta. Kotun ta tabbatar da hukuncin da kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe da kotun ɗaukaka ƙara suka yanke,” in ji Mai Shari’a Garba.
Wannan hukunci ya tabbatar da cewa Sanata Okpebholo na jam’iyyar APC ne, halastaccen wanda ya lashe zaɓen gwamnan Jihar Edo na shekarar 2024.
PDP ta zargi cewa an yi maguɗi a zaɓen, inda ta nemi a soke sakamakon.
Amma kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe da kotun ɗaukaka ƙara suka yi watsi da ƙorafinta, wanda ya sa suka kai ƙarar zuwa Kotun Ƙoli.
Da wannan hukunci, an rufe duk wata shari’a da ta shafi zaɓen gwamnan Jihar Edo.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp