Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja a ranar Juma’a ta tabbatar da Gwamna Bala Muhammad na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
Kotun mai alkalai uku sun amince da nasarar da Bala Muhammad ya samu a hukuncin da suka yanke kan ɗaukaka ƙarar da dan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar APC, Ambasada Sadique Abubakar ya shigar da ke kalubalantar nasarar Bala Muhammad da kuma hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe ta yanke.
- Cire Kashi 40 Na Kudin Shigar Jami’o’i Zai Kassara Su – ASUU
- Zan Tabbatar Da Ayyukan Sarakuna A Tsarin Mulki – Tinubu
Da ya ke tofa albarkacin bakinsa kan hukuncin, mataimakin gwamnan jihar Muhammad Auwal Jatau, ya nuna gayar farin cikinsu bisa wannan matakin tare da misalta a hakan a matsayin tabbatar wa al’umman jihar Bauchi abun da suka zaba.
A wata sanarwa da hadiminsa a bangaren watsa labarai, Malam Muslim Lawal ya fitar a ranar Juma’a, ya ce, wannan hukuncin ya tabbatar da nasarar da Bala Muhammad ya samu, kuma hakan zai kara ba su dama da azamar ci gaba da shimfida ayyukan raya jihar Bauchi ne.
Idan za a tuna dai, hukumar zaɓe INEC tun da farko ta bayyana Bala Muhammad na PDP da cewar ya samu kuri’u 525, 280 a zaben 2023 lamarin da ya ba shi damar zarcewa a karo na biyu, yayin da ya kayar da babban abokin karawarsa na APC Sadique Baba Abubakar da ya samu kuri’u 432, 272 yayin da kuma dan takarar jam’iyar NNPP, Halliru Dauda Jika ya samu ƙuri’u 6,496 kacal.