Kotun koli ta jingine zaben da aka yi wa tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau a matsayin Sanatan da aka sake zaba da zai wakilci Kano ta Tsakiya a zaben ranar 25 ga watan Fabirairu 2023 a jam’iyyar NNPP.
Kotun mai makon sunan Shekarau, ta tabbatar sunan Rufai Hanga a matsayin sanatan da aka zaba a mazabar ta Kano ta tsakiya a karkashin inuwar jamiyyar NNPP.
- Kungiyar Mata Lauyoyi Na Bukatar Sanya Mata A Gaba A Fannin Fasaha Da Kirkire-Kirkire
- An Fara Gwagwarmayar Neman Shugabancin Majalisun Kasa
A cikin hukuncin kotun biyo bayan daukaka karar da INEC ta yi, kotun kolin ta kuma tabbatar da hukuncin da kotun tarayya da na kotun daukaka kara suka yanke a baya na cewa, Rufai Hanga ne ya lashe zaben.
Mai shari’a alkali Uwani Aba-Aji ne ya tsara yanke hukuncin inda kuma mai shari’a alkali Emmanuel Agim ya gabatar da yanke hukuncin, inda ya ce INEC ba ta hurumin da kwararan hujjoji inda kutun ta yi watsi da daukaka karar ta INEC.
A hukuncin na baya da kotun tarayya da na kotun dauka kara sun yanke hukuncin cewa, dan takarar sanata a NNPP na Kano ta tsakiya bayan Shekarau ya fice daga cikin NNPP da kuma tsaya wa takarar sanatan saboda wasu lamura na siyasa da ya yi zargin akwai a tsakanin sa da NNPP, mai makon ya yi biyayya da umarnin kotun tarayya, INEC ta daukaka kara kan hukuncin amma bata samu nasara ba.
Hakazalika, ganin cewa, INEC ba ta gamsu da hukuncin ta garzaya zuwa kotun koton koli domin kalubalantar hukuncin da ya tabbatar da Rufai a matsayin halartaccen dan takarar sanata a NNPP.