ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kungiyar Mata Lauyoyi Na Bukatar Sanya Mata A Gaba A Fannin Fasaha Da Kirkire-Kirkire

by Khalid Idris Doya
4 years ago
Kungiyar Mata Lauyoyi

Wata Kungiyar mata lauyoyi ta kasa ‘International Federation of Women Lawyers’ (FIDA), ta nuna bukatar da ke akwai na sakarwa mata cikakkiyar dama domin su baje baiwar fasahar da Allah ya huwace musu ta hanyar amfani da fasahar zamani, kimiyya da kuma kirkire-kirkire.

A wata sanarwar da shugabar kungiyar reshen jihar Bauchi, Fatima Abubakar ta fitar domin raya ranar mata ta duniya na wannan shekarar mai taken Maida hankali kan rawar da kirkire-kirkire da fasaha ke takawa wajen inganta daidaiton jinsi a tsakanin maza da mata.

  • ‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa 2 Da Ceto Mutum 1 A Bauchi
  • An Fara Gwagwarmayar Neman Shugabancin Majalisun Kasa

FITA ta ce, lura da yadda zamani ke tafiya a halin yanzu, kirkira da fasaha su ne hanyoyi da suka fi dace a maida hankali a kai. Kana, sannu a hankali fasaha na shiga cikin harkokin rayuwa na yau da gobe, ayyukanmu, sadarwa, hada-hadar cinikayya, koyo da koyarwa da kuma sha’anin sarrafa kudade.

ADVERTISEMENT

Kazalika, kungiyar ta nuna damuwarta kan yadda mata kalilan ke samun dama wajen baje baiwar da Allah ya musu na fasaha a wurare daban-daban.

“Mun yi la’alari da kalubalen da mata ke fuskanta a wannan fannin saboda yadda aka saba tun da farko bisa al’adar da ya dakile mata musamman iyaye.

LABARAI MASU NASABA

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota

‘Yansanda Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Damfarar Wayar Salula A Jihar Adamawa

“Fasaha ya bude sabon babi wa mata a bangaren aiki domin kuwa su na samun damar tafiyar da harkokinsu na kashin kai da kuma na ayyukansu da shi.

“Ko a lokacin annobar Korona da ya tilasta wa mata aiki daga gida. Mun jinjina wa kokarin mata ta yadda suka tashi suka koya suka kuma rungumi amfani da kimiyya da fasaha.”

FIDA ta kara da cewa, bisa rungumar kimiyya da mata suka yi, hakan ya bude musu sabbon babin koyon ilimi ta yadda suke iya amfani da shiga dauran darussan kwasa-kwasai ta hanyar yanar gizo a fadin duniya, “Hakan ya bude damarmaki sosai masu kyau da nagarta ga ‘yan uwa mata da ke taimaka mana a fannonin aikinmu sosai.”

Don haka FIDa ta ce, akwai gayar bukatar a cire dukkanin wani banbance-banbancen da ke dakile mata daga shiga a dama da su a harkar kimiyya, kungiyar tana mai cewa babu wani nau’in fasaha da wani namiji zai iya shiga a dama da shi da mata ma ba za su iya yin hakan ba.

Fatima ta karfafi mata a Nijeriya da suke shiga a dama da su a dukkanin wani gasa ko gabzatar gwajin fasaha da ake sanyawa a ko’ina a duniya domin bai wa mata cikakken dama da kwarin guiwar amfanuwa da kimiyya tare da kara samun damarmaki a fannin. Ta kuma nemi masu ruwa da tsaki da suke daukan nauyin mata wajen neman ilimi a fannin kimiyya, Fasaha da lisasafi (STEM) domin karfafa wa mata masu tasowa guiwa.

Kazalika, kungiyar ta ce akwai kuma bukatar cigaba da wayar wa yara mata alfanun da kimiyya ke da shi a garesu da cigaban al’umma.

Daga bisani kungiyar ta yi sha’awar a shawo kan banbance-banbance da ake da su a tsakanin maza da mata a fannin kimiyya da Fasaha domin Mata na suke samun cikakken damar guragwn ayyukan yi da bada nasu gudunmawar a cikin al’umma.

Kungiyar Mata Lauyoyi
Khalid Idris Doya
+ postsBio
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Yaro Ya Harbe Kansa Har Lahira Bayan Mafarauci Ya Yi Sakaci Da Bindigarsa A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    An Kama Mutane 5 Da Sassan Jikin Ɗan’Adam Za Su Yi Tsafi A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Tsohon Mai Neman Takarar Gwamnan Bauchi, Bala Jibrin, Ya Fice Daga APC Kan Zargin Ɗoki-ɗora

MASU ALAKA

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota
Kotu Da Ɗansanda

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota

July 18, 2026
An Kama Matashi A Kano Kan Zargin Kashe Abokinsa
Kotu Da Ɗansanda

‘Yansanda Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Damfarar Wayar Salula A Jihar Adamawa

July 18, 2026
Disu
Kotu Da Ɗansanda

IGP Disu Ya Hana Jami’an Ƴansanda Yin Amfani Da TikTok Da Instagram Da Sauransu

June 26, 2026
Next Post
Kotun Koli Ta Umarci INEC Ta Maye Sunan Shekarau Da Hanga

Kotun Koli Ta Umarci INEC Ta Maye Sunan Shekarau Da Hanga

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.