Kotun sauraren kararrakin zabe da ke zamanta a Kano ta tabbatar da zaben, Abdulmumin Jibrin Kofa, na jam’iyyar (NNPP) a matsayin zababben dan majalisar wakilai daga mazabar Kiru/Bebeji bayan watsi da karar da Sa’idu Kiru na jam’iyyar (APC) ya shigar gabanta kan rashin isassun shaidu.
A ranar Laraba ne kotun ta yi watsi da karar da Sa’idu Kiru ya shigar inda ya ke korafin cewa jam’iyyarsa ta yi watsi da sahihancin zaben dan majalisar wakilai na Kiru/Bebeji, Abdulmumini Jibrin Kofa na NNPP.
- Hukuncin Zaben Gwamnan Kano: Magoya Bayan NNPP Da APC Sun Dukufa Addu’o’i
- NNPP Ta Zargi Gwamnatin Ganduje Da Kai Hare-Hare Kan Mazauna Kano
Alkalan Kotun uku da mai shari’a, Ngozi Flora, ta jagoranta sun bayyana cewa takardun da bangarorin biyu suka gabatar a gaban kotun sun nuna cewa, Abdulmumini Jibrin Kofa, ya ajiye mukaminsa na babban sakataren hukumar gidaje ta tarayya kwanaki 30 gabanin gudanar da zaben 2023.
An kori wannan mai kara ne saboda rashin cikakkun shaidu.