Babbar kotun tarayya ta kori dan majalisa mai wakiltar mazabar Mubi ta Kudu a majalisar dokokin Jihar Adamawa, Honarabul Musa Umar Bororo.
Babbar kotun tarayyar da ke zaune a Yola a ranar Litinin, ta umarci dan majalisar da ya bar kujerarsa ba tare da bata lokaci ba saboda ficewa daga jam’iyyar da ya lashe zaben majalisar a cikinta.
- Dalilin Da Ya Sa Kotu Ta Dakatar Da Ayu Daga Shugabancin PDP
- ‘Yan Nijeriya Za Su Yi Kewar Buhari Idan Ya Sauka Daga Mulki –Garba Shehu
A watan Afrilun bara ne dai Bororo ya fice daga jam’iyyar adawa ta APC a jihar ya koma jam’iyyar PDP mai mulki.
Babbar kotun da ke karkashin mai shari’a Saleh Kogo, ta yanke hukuncin cewa Bororo wanda ya shiga majalisa a karkashin jam’iyyar APC, bai kamata ya koma PDP ya ci gaba da zama a kan mukaminsa ba.
Sai dai mai shari’a Kogo, ya yi watsi da karar da aka shigar a gaban memba mai wakiltar Mubi ta Arewa, Hon Shuaibu Dan Musa da memba mai wakiltar Fufure/Gurin, Hon Shuaibu Babas wanda shi ma ya sauya sheka daga APC zuwa PDP a lokuta daban-daban.
Ya ce jam’iyyar APC ta kasa tabbatar da shari’ar da ta ke a kan mutanen biyu.
A watan Oktoban shekarar da ta gabata ne dai shugabannin jam’iyyar APC na jihar suka maka ‘yan majalisar uku a gaban kuliya saboda sun fice daga jam’iyyar PDP, inda suka bukaci kotun da ta karbe kujerunsu.