Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta bayyana cewa lokaci ya yi da ‘yan bindiga da ke addabar Arewacin Nijeriya su daina kashe mutane su kuma miƙa wuya.
Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ne ya faɗa hakan a hirarsa da BBC Hausa, inda ya ce gwamnatin ta samu nasarar rage hare-haren ta’addanci da na ‘yan bindiga.
- Gwamnonin Nijeriya Sun Yi Ta’aziyyar Waɗanda Suka Rasu A Ambaliyar Ruwa A Adamawa
- Babu Wata Karamar Hukumar Da Ke Ƙarƙashin Ikon Ƴan Ta’adda A Filato -Gwamna Mutfwang
Ya ce a da ana kai wa hari a gidajen yari da jirgin ƙasa da sansanonin sojoji, amma yanzu an daƙile hakan tun bayan da wannan gwamnati ta hau mulki.
Ribadu ya ce: “Muna ganin waɗanda suke ta’addanci lokaci ya yi da za su tsaya su daina.”
Ya ƙara da cewa gwamnati ta kashe shugabannin ‘yan bindiga kimanin 300.
Har ila yau, Ribadu ya ce yanzu mutane suna iya zuwa gonakinsu a wuraren da a baya ba a iya shiga saboda barazanar ‘yan bindiga.
Sai dai duk da wannan ikirari, har yanzu wasu yankunan kamar Zamfara, Benuwe da Filato na fama da hare-haren ‘an bindiga da rikicin ƙabilanci.
A ƙarshen makon da ya gabata, ‘yan bindiga sun kashe mutane a Kauran Namoda a Jihar Zamfara.
Sannan ƙungiyar Boko Haram har yanzu na ci gaba da zama barazana a Arewa Maso Gabas.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp