Ministan Ayyuka, Sanata Nweze David Umahi, ya ba wa ƴan kwangilar da ke gudanar da ayyukan gaggawa na hanyoyi 260 na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu GCFR wa’adin watanni uku don kammala ayyukan kamar yadda tsarin dokar ba da ayyukan kwangila ya tana da na Ma’aikatar Aiyuka ta Tarayya, inda ta buƙaci hakan ko kuma su fuskanci dakatar da kwangilar baki ɗaya.
An bayar da wannan wa’adin ne a yayin wani taro da aka yi da mahukuntan ma’aikatar da ‘yan kwangilar da ke gudanar da ayyuka daban-daban da kuma masu kula da ayyuka na tarayya da aka gudanar a shelƙwatar ma’aikatar da ke Abuja.
- Wakar Kidaya: Aisha Humaira Ta Nemi Al’umma Su Daina Tsangwamar Mawaki Rarara
- Majalisa Za Ta Binciki Zargin Badakalar Naira Tiriliyan 2 A Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya
Haka Kuma ya ce “Ayyukan titin na gaggawa an tsara su ne a cikin ƙarin kasafin kuɗi na 2023 da nufin kawo ɗauki cikin gaggawa kan sassan da suka gaza gaba ɗaya na manyan titunan gwamnatin tarayya a faɗin Nijeriya.
Ministan dai ya bayyana kimanin ‘yan kwangila 37 ne da basu samu ci gaba ko kaɗan da aikin tun lokacin da aka bayar da kwangilar tare da gargadin cewa dole ne irin waɗannan ‘yan kwangilar su tabbatar da sun koma wuraren da suke gudanar da ayyukan su zuwa ranar 10 ga watan Yuli 2024 ko kuma su fuskanci hukumcin rasa kwangilar, Inji shi.
Ya ce, “Idan wa’adin da aka ɗiba na miƙa ayyukan hanyar ya yi duk wani ɗan kwangila ya kasa cimma wa’adin aikin, za a dakatar da aikin ne ta hanyar zubewar lokaci domin kwangilar na tsawon watanni 3 ne.