Sarkin Kudun Gatawa, Alhaji Muhammad Bawa, wanda aka sace kwanaki 23 da suka gabata a jihar Sokoto, ya roƙi gwamnati da Majalisar Sarkin Musulmi da su taimaka wajen biyan kuɗin fansar da masu garkuwar suka nema kafin wa’adin da suka gindaya ya cika.
A cikin bidiyon da aka saki a ƙarshen mako, an ga basaraken cikin yanayi na tashin hankali, sanye da tufafin da suka jiƙe da jini kuma ɗaure da sarƙoƙi. Ya bayyana cewa ya yi wa gwamnati hidima tsawon shekaru 74, ciki har da shekaru 45 a aikin gwamnati, don haka yanzu lokaci ya yi da gwamnati za ta taimaka masa a wannan mawuyacin hali.
- Garkuwa: Sarkin Gobir Ya Bukaci Agajin Gaggawa Daga Gwamnatin Sakkwato
- CDD Ta Soki NBC Kan Cin Tarar Trust TV Da Wasu Miliyan 20
Basaraken ya kuma bayyana cewa akwai kusan mutane 86 da ake tsare da su tare da shi a hannun masu garkuwar. Ya roƙi gwamnati, iyalansa, da duk wanda zai iya taimakawa da su gaggauta ɗaukar mataki don ceto rayuwarsa. Alhaji Bawa ya yi wannan kiran ne cikin muryar roko da fatan samun ceton rayuwarsa kafin lokaci ya ƙure.
Dangane da lamarin, wani dan Majalisar Dokoki ta Jihar Sokoto, Honarabul Aminu Boza, ya tabbatar da cewa mutumin da ke cikin bidiyon shi ne basaraken da aka sace.
Iyalin Sarkin sun nuna damuwa da takaici kan yadda suka sanar da hukuma, amma har yanzu ba a sami cikakkiyar kulawa ba. Sun bayyana cewa duk da kokarin tattaunawa da masu garkuwar da suka yi, waɗanda suka sace shi sun nace sai gwamnati ta shiga lamarin kafin a sako shi.