Jam’iyyar ADC ta zargi hukumar EFCC na yin son zuciya tare da yin aiki a matsayin kayan aikin siyasa ga jam’iyyar mai mulki APC. Jam’iyyar ta gargaɗin cewa irin wannan mataki yana rage ingancin yaƙin da ake da cin hanci da kuma rage amincewar jama’a.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Mallam Bolaji Abdullahi, ya fitar, ADC ta bayyana cewa ayyukan EFCC na baya-bayan nan, ciki har da buɗe tsofaffin shari’o’i da kuma maida hankali kan ƴan adawa, sun nuna halayyar kamar ta “mai aiwatar da umarnin siyasa” maimakon hukuma mai aiki da gaskiya. Ta kuma zargi hukumar da kiran wasu shugabannin adawa kan shari’o’in da suka dogara da tsoffin zarge-zarge na siyasa.
- UEFA Ta Ci Tarar Lamine Yamal Da Lewandowski Kan Karya Dokar Shan Ƙwayar Ƙara Kuzari
- Yanzu Haka Muna Bincikar Gwamnoni 18 – Shugaban EFCC
ADC ta jaddada cewa an kafa EFCC ne domin tabbatar da adalci ta hanyar aiwatar da doka a kan kowane ɗan Nijeriya ba tare da wariya ba, amma yanzu wannan hangen nesan da aka yi ya lalace. Ta zargi hukumar da barin shari’o’in da suka shafi abokan APC su shuɗe ba tare da kulawa ba, yayin da take tsananta bincike kan ƴan adawa, lamarin da ke ƙara tabbatar da ra’ayin cewa alaƙa da jam’iyya mai mulki ne ke tantance wanda za a bincika.
Jam’iyyar ta yi kira ga ƴan Nijeriya, da ƙungiyoyin farar hula da kafafen yaɗa labarai da su ƙi amincewa da duk wata alama ta mulkin kama-karya, ta kuma tunatar da EFCC cewa hukuma ce ta ƙasa wadda ake ɗaukar nauyinta daga harajin jama’a, ba sashi a jam’iyya mai mulki ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp