Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya roki ‘yan Nijeriya da su yi hakuri da gwamnatin shugaba Bola Tinubu.
Shettima ya yi wannan roko ne a ranar Asabar da ta gabata a garin Kafur na jihar Katsina a wajen kaddamar da wani shiri na karfafawa wanda babban mai taimakawa shugaban kasa na musamman kan harkokin siyasa Ibrahim Masari ya dauki nauyi.
- Shettima Zai Kaddamar Da Cibiyar Horaswa Da zaƙulo Hazikan Matasa A Gombe
- Kashim Shettima Ya Mayar Da Martani Kan Tsadar Rayuwa
Mataimakin shugaban kasar ya jaddada cewa shugabanci ya shafi nuna tausayi da goyon bayan jama’a.
Ya ce shugaban kasar yana da muradin ci gaban ‘yan Nijeriya a zuciyarsa da kuma kyawawan tsare-tsare na inganta yanayin rayuwarsu.
“Shugabanci ya shafi nuna tausayawa da goyon baya ga jama’a.
“Shugaban kasa yana da muradin ci gaban al’ummar wannan kasa mai girma a zuciyarsa. Cewar Shettima.