Titi Atiku, mai dakin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP Alh. Atiku Abubakar, ta sheda wa daukacin matan Nijeriya cewa, ita za su zarga in har mijinta ya gaza cika alkawuran da ya dauka a yayin yakin neman zabensa in ya lashe takara ta shugaban kasa.
Titi ta kuma yi alkawarin cewa, idan Atiku ya zama shugaban kasar ba zai mayar da yankin kudu maso yamma saniyar ware ba, inda ta yi nuni da cewa, kada wa Atiku kuri’ar su, tamkar zabar dan yankinsu ne, bayarabe.
Titi wacce ta bayyana hakan a Abeokuta a taron da ta yi da matan Ogun, inda ta yi nuni da cewa , in aka zabi Atiku a matsayin shugaban kasa za ta zama matar shugaban kasa ta farko data fito daga kabilar yarbawa.
Ta ce, tana da yakinin in har aka zabi Atiku, zai iya kawar da talauci da magance kalubalen rashin tsaro a kasar nan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp