Wakilinmu ya samu labari daga hukumar kididdiga ta kasar Sin yau Laraba cewa, kudin da aka kashe kan bincike da gwajin kimiyya na Sin wato R&D, ya ci gaba da bunkasa, kuma karfin zuba jari na ci gaba da karuwa.
A shekarar 2023, Sin ta zuba jarin yuan triliyan 3.33571 kan ci gaban bincike da gwajin kimiyya, wanda ya karu da kashi 8.4 bisa dari a kan shekarar 2022. A shekarar 2023, adadin kudaden gudanar da bincike kan ilmomin tushe na kasar ya kai yuan biliyan 225.91, wanda ya karu da kashi 11.6 bisa dari a kan shekarar 2022.
Idan aka yi la’akari da yankuna, akwai larduna da birane bakwai da karfin zuba jarinsu a fannin ya zarce matsakaicin karfi na dukkan sassan kasar, wato Beijing, Shanghai, Tianjin, Guangdong, Jiangsu, Zhejiang da kuma Anhui.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp